Akalla mutum 11 ne wasu ’yan bindiga suka sace a kauyen Illela da ke Karamar Hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, da misalin karfe 4:00 na safiyar Alhamis ne ’yan bindigar suka auka wa kauyen, sannan suka sace mutanen, cikin su har da wata tsohuwa mai kimanin shekarar 70 mai suna Zainab Adamu.
Majiyar, ta shaida cewa, tsohuwar ta rasu ne a hannun ’yan bindigar, yayin da biyu daga cikin mutanen da aka sace suka kubuta daga inda aka boye su.
Har ila yau, daga cikin mutanen da aka sace har da ɗan Dagacin garin Zip.
Dagacin, Alhaji Uba, ya shaida cewa, dan nasa mai suna, Buhari na daga cikin mutanen da aka sace a yayin harin.
Sai dai ya ce, har har yanzu ya na hannun wadanda suka sace shi.
Alhaji Uba ya ce, ’yan bindigar dai sun bukaci a biya su kudi har Naira miliyan 70 a matsayin kudin fansa.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar harin, ko da yake bai yi karin haske a kai ba.