An yi garkuwa da wata matar aure mai suna Hajiya Kara’atu Tanimu a Jalingo babban birnin jihar Taraba.
Sace ta na zuwa ne mako guda bayan da aka yi garkuwa da matar wani babban Sufeton ‘yan sanda, CSP a unguwar Mile-Six da ke cikin birnin.
Da yake tabbatar da sace matar a ranar Juma’a, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman, ya ce lamarin ya faru ne a unguwar Nasarawo da ke Jalingo a daren Alhamis.
“An tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutane a yankin Nasarawo da ke Jalingo. Wasu mahara ne suka mamaye gidan wani Alhaji Taminu Rabiu.
“Ko da yake Tanimu ba ya gida, ya yi tafiya zuwa Saudiyya, amma a lokacin da suka zagaya cikin gidansa, suka yi garkuwa da matarsa, Hajiya Karatu Tanimu da kuma yayansa Abdulhameed Rabiu,” in ji Usman.
Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun kuma yi awon gaba da wayoyin hannu da kuma kudi N11,000.
Sai dai Usman ya tabbatar da cewa ‘yan sandan na kan bin maharan.
Har ila yau, da ke tabbatar da rahoton, wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce masu garkuwa da mutanen sun kai farmaki yankin ne a daren jiya, inda suka bace tare da Hajiya da kuma kanin Alhaji Rabiu.
Ya bukaci gwamnatin jihar da ta hada kai da jami’an tsaro wajen ceto wadanda lamarin ya shafa.
Mazauna garin da suka zanta da DAILY POST sun bayyana damuwarsu kan yadda masu garkuwa da mutane ke yin gaggawar kwace babban birnin jihar.


