Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, ta tabbatar da sace wata mata mai juna biyu, Rahila Da’u, mai shekaru 25 a kauyen Gizaki da ke unguwar Lusa a karamar hukumar Bogoro a jihar.
Kakakin Rundunar, SP Ahmed Wakil wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Bauchi, ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 16 ga watan Yuli.
Ya ce, an kai rahoton faruwar lamarin ne a ofishin ‘yan sanda na Bogoro kuma kwamishinan ‘yan sandan, Umar ya bukaci jami’an da su yi duk mai yiwuwa don ceto wanda abin ya shafa.
Ya kara da cewa, jami’an mu ciki harda Batruan ‘yan sanda, suka jagorantanci ziyarci wurin, inda suka kwato harsasai 5 da babu kowa a ciki da masu garkuwa da mutane suka harba.
Sai dai ya tabbatar da cewa, ‘yan sanda na kan gaba wajen tabbatar da cewa, an ceto wanda abin ya shafa ba tare da wani rauni ba.
A halin da ake ciki, shugaban karamar hukumar Bogoro, Mista Iliya Habila, ya yi kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin al’ummar yankin da su kara sanya ido tare da karfafa hanyoyin tsaro na cikin gida domin dakile kwararar baki zuwa yankunansu.
Ya ce, hakan zai kaucewa afkuwar satar mutane a nan gaba da sauran laifuka.