Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wata mata mai juna biyu a unguwar Lema da ke Mando daura da makarantar horas da sojoji ta (NDA) da ke Zaria a jihar Kaduna.
An yi garkuwa da wasu mutane bakwai a lokacin da ‘yan bindigan suka shiga gidaje uku da misalin karfe 1:00 na safiyar Lahadi.
Daya daga cikin mazauna unguwar Musa Danladi ya ce dukkansu suna tsoron fita daga gidajensu saboda harbin bindiga.
“Sun zo ne da misalin karfe 1:00 na safe, suka tafi da mazauna garin takwas ciki har da wata mata mai juna biyu da ta zo ziyarar mahaifiyarta da ba ta da lafiya a unguwar. Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yan bindiga za su kai wa al’ummarmu hari ba,” inji shi.
Sauran mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta kawo musu dauki.
Har yanzu dai gwamnati ba ta ce uffan ba kan lamarin, sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya ce zai ji cikakken bayani game da lamarin, a cewar Daily Trust.