Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da wani limamin cocin Katolika, Rev Fr Jude Kingsley Maduka na cocin Katolika na Okigwe a jihar Imo.
Maduka, wanda aka nada shi sama da shekaru goma da suka gabata, shine limamin cocin Christ the King Parish, Ezinnachi/Ugwaku, karamar hukumar Okigwe, jihar Imo.
Shugaban cocin Katolika kuma sakataren cocin Katolika na Okigwe, Rev Fr Iwuanyanwu, ya bayyana haka ranar Asabar a jihar.
Fr Iwuanyanwu ya ce “An yi garkuwa da shi ne daga shafin sa na New Adoration da ke kauyen Ogii a karamar hukumar Okigwe a lokacin da yake duba sabon wurin.”