Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun yi garkuwa da basaraken Owa-Onire a gundumar Kwara ta Kudu a jihar Kwara.
DAILY POST ta samu labarin cewa an yi garkuwa da shi tare da matarsa da direban sa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar DAILY POST a ranar Asabar.
Okasanmi ya bayyana cewa yanzu haka mutane biyu da ake zargi suna hannun ‘yan sanda kan lamarin.
Ya bayyana cewa an ceto matar sarkin, yayin da ake ci gaba da kokarin ceto sauran biyun da suka rage.
A cewar Okasanmi, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Paul Odama, ya aike da tawagar masu bincike tare da ‘yan banga zuwa wurin.
Kakakin ya ce za a bayyana cikakken rahoto da zarar an kammala bincike kan lamarin.
Wannan dai shi ne karo na farko da aka yi garkuwa da shi tun bayan da sabon kwamishinan ‘yan sandan ya hau ofishin a watan da ya gabata.