fidelitybank

An yi garkuwa da Ango da Amarya a Katsina

Date:

Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu sabbin ma’aurata bayan kashe jami’an sa-kai biyu a wani hari da suka kai unguwar Shola da ke birnin Katsina.

A cewar mazauna unguwar ‘yan bindigar sun far mu su ne da misalin ɗaya da minti ashirin da biyar na dare, kuma sun shafe sa’a guda su na harbe-harbe.

Sun shaida cewa ‘yan sa-kai sun rasa rayukansu ne a kokarin hana garkuwa da ma’auranta, sannan an jikkata wasu daga cikinsu.

Rahotanni na cewa dole ta sanya masu aikin sa-kai janye jiki bayan sun fahimci cewa ‘yan bindigar sun fi karfinsu.

Wani mazaunin unguwar ta Shola da ke cikin Katsina ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun shiga unguwar ne bisa babura jiya dauke da bindigogi suna harbe-harbe.

Mutumin yace ‘yan bindigar sun fasa wani gida ta baya suka shiga. Al’amarin dai yayi sanadin mutuwar mutum biyu sanann mutum biyu suka jikkata. In ji BBC.

Ya kuma ce baya ga ma’auratan akwai mutane da dama da aka sace, sai dai bai san adadi ba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da mahara ke aukawa unguwar Shola ba, ko fiye da wata guda ma ‘yan bindiga sun shiga yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar wannan hari, inda ya ce jami’ansu sun dukufa don kuɓutar da amarya da angon.

Bugu-da-kari SP Gambo ya ce sun kubutar da wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su a kauyen Tandama cikin karmar hukumar Danja, bayan wani samame da suka kai maboyar ‘yan bidiga.

Haka kuma, ya ce a yankin karamar hukumar Safana ma, sun yi nasarar kashe wani kasurgumin dan fashin daji Albdulkarim Faca-Faca da mutanansa bakwai a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin yaki ya yi akan maboyarsu

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp