Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun hadu a tashar harba kumbo ta Vosto-chny da ke gabashin Rasha inda za su tattauna.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Telegram na gwamnatin Kremlin, ya nuna shugabanni biyu na musabaha.
Mista Kim, wanda ya shiga Rasha da jirgin kasa mai sulke a safiyar ranar Talata, ya samu rakiyar manyan hafsoshin tsaronsa a ziyara ketare ta farko da ya ke kai wa a cikin shekaru hudu.
Wakiliyar BBC da ke aiko rahoto daga can ta ce kada ku yi tunanin za a samu bayanai kan duk wata haramtacciyar yarjejeniyar da za su ƙulla.
Kasahen duniya dai na nuna rashin gamsuwa da sabuwar alaƙar wadannan kasashe biyu.


