fidelitybank

An yi gamo tsakanin Putin da shugaban sohin haya na Wagner

Date:

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gana da shugaban sojojin hayar Rasha na Wagner, Yevgeny Prigozhin bayan gazawar kungiyar a watan da ya gabata, in ji fadar Kremlin.

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya kara da cewa Prigozhin wanda ke jagorantar kungiyar sojojin haya na Wagner na daga cikin mutane 35 da aka gayyata zuwa taron da aka yi a birnin Moscow.

Ya ce shugaba Putin ya yi bayani kan yadda yaƙin Ukraine ke gudana da kuma boren sojojin haya.

Tawayen da suka kaddamar a ranar 23 ga watan Yuni ya É—auki tsawon sa’o’i 24.

A karkashin yarjejeniyar, an yi watsi da tuhumar Prigozhin kuma an yi masa tayin koma wa Belarus.

An yi ta ce-ce-ku-ce tsakanin jama’a tsakanin Wagner da ma’aikatar tsaron Rasha game da gudanar da yakin. Prigozhin dai ya sha zargin ma’aikatar da gazawa.

Sai dai a ranar Litinin, Mista Peskov ya ce shugaban Wagner na cikin kwamandojin da aka gayyata zuwa Kremlin kwanaki biyar bayan rugujewar rikicin.

Kamfanin dillancin labaran Interfax ya ambato Mista Peskov yana cewa “Shugaban ya yi bayani akan abubuwan da kamfanin yayi a fagen daga.

A cewar kakakin, ya ce Prigozhin ya shaida wa Mista Putin cewa Wagner ta goyi bayansa ba tare da wani sharaÉ—i ba. Ba a dai san inda shugaban na Wagner yake ba.

A ranar Alhamis É—in da ta gabata, shugaban Belarus Alexander Lukashenko – wanda ya kulla yarjejeniya ta kawo karshen tashin hankali – ya ce Prigozhin yana Æ™asar Rasha.

nigeria daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp