fidelitybank

An yi faɗan ƙabilanci a jihar Ondo

Date:

l’ummar Ogbese da ke karamar hukumar Akure ta Arewa a Jihar Ondo, ta shiga cikin tashin hankali, bayan wani kazamin rikici da ya barke tsakanin Fulani da Hausawa mazauna yankin.

An ce mutum daya ya mutu a rikicin tare da jikkata mutane da dama tare da lalata dukiyoyi.

An tattaro cewa rikicin da ya faro tun a yammacin ranar Talata ya yi kamari ne da safiyar Laraba, inda aka kona wasu shaguna na ‘yan Arewa a babbar kasuwar al’umma.

A lokacin da aka gabatar da wannan rahoto, har yanzu ba a san ainihin dalilin da ya haddasa rikicin ba, amma an gano cewa unguwar na cikin tashin hankali.

Sai dai wani dan unguwar ya yi ikirarin cewa rikicin ya samo asali ne daga wata hatsaniya tsakanin wani Bafulatani da ke zaune a dajin da kuma wani Bahaushe da ke zaune a unguwar a kan tabar wiwi da aka fi sani da hemp Indiya.

Kakakin ‘yan sandan, Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da cewa shaguna 8 ne aka kone, amma ta musanta rahoton rikicin kabilanci.

sun news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp