An samu tashin hankali a karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna, yayin da wasu ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan Ansaru suka yi artabu da bindiga.
‘Yan kungiyar Ansaru dai na yin wa’azi ga jama’ar yankin ne a lokacin da ‘yan bindigar suka far wa jama’ar, inda suka rika harbe-harbe ba da jimawa ba, inda suka kashe mutanen kauyen biyu.
Lamarin dai kamar yadda aka bayyana wa Aminiya ya ce, ‘yan bindigar sun shiga kauyen Damari da ke karkashin gundumar Kazage da ke yankin Gabashin karamar hukumar da nufin fatattakar ‘yan ta’addan daga kauyen.
An tattaro cewa, kungiyar Ansaru ta kwace yankuna da dama a Gabashin karamar hukumar da sunan jagorantar hare-haren ‘yan bindiga.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban kungiyar cigaban Masarautar Birnin-Gwari (BEPU), Ishaq Usman Kafai, ya shaidawa manema labarai cewa, an dauki tsawon sa’a guda ana rikicin tsakanin kungiyoyin biyu.
A cewarsa, ‘yan kungiyar ta Ansaru wadanda su ma dauke da muggan makamai sun yi galaba a kan ‘yan bindigar wanda hakan ya sanya su ‘yan bindigar suka koma kauyen.
Duk da haka, a cewar Kafai, an samu asarar rayuka da dama yayin arangamar.
“An samu barna a yayin arangamar; an kona wani shago; motoci biyu sun kone; An kona wani Asibiti mai zaman kansa. ‘Yan bindigar ma sun kashe wasu ‘yan unguwar (ma’aikata) guda biyu yayin da ‘yan fashin ke guduwa cikin dajin,” inji shi.
Ishaq ya shaidawa kafar yada labarai cewa asibitin ya kone bisa kuskure sakamakon gobarar da ta tashi daga wata mota da ta kone.
Ya kara da cewa, ba a iya tantance adadin da aka kashe tsakanin ‘yan bindigar da ‘yan Ansaru ba amma ya ce mutanen yankin sun yaba wa ‘yan kungiyar ta Ansaru saboda kare garin daga harin ‘yan bindigar.
Naija News ta samu cewa daruruwan mazauna garin da suka hada da mata da kananan yara sun tsere daga garin yayin harin.
Rahoton ya ce ‘yan kungiyar ta Ansaru sun ci gaba da wa’azin bayan fafatawar inda suka shawarci jama’a da su mallaki makamai don kare kansu daga makiya tare da yaki da gwamnati domin tabbatar da abin da suke kira daular Musulunci.