An shiga ruɗani a Kaduna bayan da ƴan sanda suka yi kokarin tarwatsa mambobin kungiyar Islamic Movement Of Nigeria wadanda aka fi sani da ‘yan Shia, wadanda ke gudanar da muzahara a tsakiyar birnin.
Mambobin kungiyar sun taru a kan shatale-talen Katsina a Ahmadu Bello Way kafin ‘yan sanda su zo da kuma kokarin tarwatsa su.
Hakan ya janyo fargaba tsakanin mazauna birnin musamman ma wadanda suke da shaguna a kusa da hanyar.
An ruwaito cewa da dama daga ciki sun rufe shagunansu saboda tsoron abin da zai faru.
‘Yan sanda a Kaduna sun ce tattakin mambobin ‘yan Shiar na yau yana a matsayin haramtacce.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ASP Mansir Hassan, ya fada wa gidan talabijin na Channels cewa mambobin kungiyar sun fito da sanyin safiyar yau rike da makamai, inda suka fara far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da sunan tattaki.
Mansir ya ce mambobin kungiyar sun far wa ‘yan sanda lokacin da suka yi kokarin tarwatsa su, inda ya ce har ta kai wasu daga cikin jami’ansu sun jikkata.
Ya ce an kama wasu daga ciki da ake zargi da rike muggan makamai kuma za a gurfanar da su gaban kotu idan aka kammala bincike.
Wanan dai ba shi ne karo na farko ba da ‘yan Shia ke gudanar da muzahara duk da haramta musu hakan da gwamnatin tarayya ta yi karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. In ji BBC.