An yi bikin ƙarin girma ga shugaban Chadi Mahamar Idriss Deby daga Janar zuwa mukamin Mashal – wanda shi ne ƙololuwar mukamin a tsarin aikin soji.
Tuni majalisar dokokin kasar ta Chadi ta amince da dokar yin ƙarin girma ga shugaban. Kuma a ranar aka yi bikin ƙarin girman a fadarsa.
A 2020 aka ayyana mahaifinsa marigayi Idriss Deby a matsayin muƙamin Mashal lokacin da yana shugaban ƙasa kafin mutuwarsa.
Mahamar Deby ya kwashe mulki ne tare da taimakon wasu manyan sojojin Chadi, kuma aka tabbatar da shi a matsayin shugaban da aka zaɓa a watan Mayun 2024, wanda ƙasashen duniya da dama ke ganin an murkushe ƴan’adawa.