fidelitybank

An yi ba ta kashi tsakanin dajin Abuja da Kaduna

Date:

Rundunar ‘yan sandan birnin Abuja, tare da haɗin gwiwa dakarun sahen yaƙi da manyan laifuka da ‘yan sanda farin kaya, da mafarauta, sun wargaza sansanonin wasu ‘yan bindiga a ƙauyen Gidan Dogo da dajin Kweti da ke kan iyakar Abuja da Kaduna.

Cikin wata sanarwar jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ‘yan sandan birnin, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce bayan samun bayanan sirri, jami’an tsaron suka kai samame dajin ranar 7 ga watan Mayu, in da suka kama mutum huɗu da suke zargi.

Sanarwar ta ce mutanen da suka kama, sun faɗa wa ‘yan sanda cewa suna cikin wani gungun masu garkuwa da mutane mai suna, ‘Mai One Million’, waɗanda suke da alhakin kai hare-hare tare da garkuwa da mutane a birnin Abuja da kewaye.

”Samamen wanda aka samu musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu, ya tilasta wa ‘yan bidigar tserewa, inda jami’an tsaro suka ƙubutar da mutanen da ‘yan bindigar ke tsare da su”, in ji sanarwar.

‘Yan sandan sun ce sun lalata sansanonin ‘yan bidigar a lokacin samamen.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan ta ce, ta sada mutanen da ta kuɓutar ɗin da iyalansu.

legit nig. news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp