A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu mutane biyar dauke da makamai suka yi awon gaba da wasu matafiya shida a kan babbar hanyar Obbo-Ile/Osi da ke karamar hukumar Ekiti a gundumar Kwara ta Kudu.
An sace su ne da misalin karfe 11:15 na safe a lokacin da suke tafiya a cikin wata mota kirar Hummer mai lamba Abuja KUJ 613 AA.
Sai dai an yi nasarar ceto hudu daga cikin matafiya shidan a ranar Talata, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya bayyana a wata sanarwa a Ilorin.
Ya ce, bayan samun bayanan, sai aka aike da tawagar ‘yan sanda na yau da kullun, tawaga Tactical, ‘yan banga da mafarauta zuwa yankin domin gudanar da bincike, ceto da kuma cafke wadanda ake zargin.
“Saboda haka, an iske motar wadanda abin ya shafa, dauke da kayan abinci a bar su, a ciki an gano wani harsashi na harsashi 7.62mm.”