Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa, dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun hallaka ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP 17 a Damasak, karamar hukumar Mobbar, jihar Borno.
Jaridar Guardian ta rawaito cewa, Garin Damasak, shelkwatar karamar hukumar Mubbar, na kusa da tafkin Yobe da kuma Tafkin Komadugu Gana River, wanda ya haɗa iyaka da jahar Neja.
Kwamandan OPHK na Arewa maso Gabashin Najeriya, Manjo Janar, Christopher Musa, shi ne ya sanar da nasarar sojojin ta samu a ranar Litinin a Maiduguri.
Kwamandan ya ce, dakarun sojijin ba su tsaya iya nan ba, sun damƙe yan ta’addan guda uku da ran su.