fidelitybank

An yanke wutar lantarkin majalisar dokokin Ghana saboda bashi

Date:

Kamfanin wutar lantarki na Ghana (ECG) ya katse wutar lantarkin majalisar dokokin ƙasar a ranar Alhamis saboda gaza biyan bashin kuɗi cedi miliyan 23 da ake bin majalisar.

Wanda yawan kuɗin ya kai dalar Amurka miliyan 1.8.

Katsewar ya kawo cikas ga muhawarar da ake tafkawa a majalisar kan jawabin da shugaban kasar ya yi, inda ƴan majalisar suka rika rera taken “Dumsor, dumsor,” wato matsalar wutar lantarki.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa duk da cewa an kunna janaretan majalisar domin samar da lantarki a lokacin, sauran sassan ginin majalisar sun kasance babu wutar a yawancin ranar.

Daraktan sadarwa na kamfanin wutar lantarki, William Boateng ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ya dauki matakin katse wutar ne saboda ƙin amincewa da majalisar dokokin kasar ta yi na “girmama sanarwar bukatar biyan bashin”.

An dai mayar da wutar lantarkin ne bayan da majalisar ta biya cedi miliyan 13 tare da yin alkawarin sasanta sauran basukan nan da mako guda.

Daraktan sadarwa na ECG ya bayyana cewa haka za su katse wutar lantarki duk wanda ake bi bashi da kuma ƙin biyan bashin. In ji BBC.

Kamfanin wutar lantarki na Ghana na fuskantar matsalar kudi, lamarin da ke janyo katsewar wutar lantarkin akai-akai daga abokan huldar da yake bi bashi a yayin da ake fama da ƙarancin wutar saboda kalubalen tattalin arziki.

nnn-news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp