An yi wa fitaccen ɗan wasan ‘Nigerian film’ John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu tiyata don cire ɗaya daga cikin kafafunsa.
Hakan na ƙunshe ne a wani bayani da aka wallafa a shafin instagram na ɗan wasan kwaikwayon, a yau Litinin.
Sanarwar ta ce, “Da misalin karfe ɗaya na rana, aka samu nasarar yi wa mahaifinmu tiyata sau bakwai don yanke kafarsa ɗaya.”
Iyalan ɗan wasan fim ɗin sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su saka Mista Ibu cikin addu’a da kuma taimaka musu.
A watan da ya gabata, wani bidiyo da Mista Ibu ya wallafa a shafinsa na Instagram ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka ga yana neman taimako da kuma addu’a wajen magoya bayansa