An ware naira tiriliyan 15.81 domin biyan basuka a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025 da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gabatar a gaban majalisa.
A yau Laraba ne Tinubu ya gabatar da kasafin na naira tiriliyan 47.9.
Haka kuma Tinubu ya ce gwamnati na hasashen tara naira tiriliyan 34.82 daga kuɗaɗen harajin da za su karɓa.
Ma’aikatun da suka fi samun kaso mai yawa sun haɗa da:
- Tsaro: Tiriliyan 4.91
- Abubuwan more rayuwa: Tiriliyan 4.06
- Kiwon lafiya: Tiriliyan 2.4
- Ilimi: Tiriliyan 3.5
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa gwamnatin ta yi ƙiyasin farashin canjin dala kan naira 1,400.