Hukumar tara kuɗin haraji ta cikin gida FIRS, ta janye daga zargin kin biyan harajin da ake yi wa Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, manyan jami’an shafin hada-hadar kuɗin intanet na Binance.
Hukumar ta yanke shawarar hakan ne bayan sun yanke hukuncin tuhumar shafin kaɗai ba tare da jami’an ba.
A ranar Juma’a ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sallami Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla na kamfanin Binance Holdings Limited bisa laifin kin biyan haraji.
Gambaryan, ɗan asalin ƙasar Amurka, da abokin aikinsa Anjarwalla sun kasance cikin waɗanda ake tuhuma da ƙin biyan haraji da gwamnatin Najeriya ke yi wa kamfanin.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta shigar da ƙara a gaban kotu, kan badakalar kudaden da ake tuhumar Binance, da suka hada da dala miliyan 35.4.
Duk waɗanda ake tuhumar sun musanta aikata yin ba daidai ba.
Gambaryan, ɗan sheakara 40, ya ci gaba da kasancewa a tsare a Abuja, yayin da hukumomi ke neman Anjarwalla bayan ya tsere daga gidan yari a watan Maris.
A farkon wannan watan ne ‘yan majalisar dokokin Amurka goma sha shida suka aika da wata wasika suna kira ga shugaba Biden da ya sanya baki wajen ganin an saki Gambaryan.