Jami’ar Bayero da ke Kano, BUK, ta umarci duk wasu dalibai da ke zama a cikin rassan makarantar guda biyu a kan su kwashe dukannin komatsen su tare da barin harabar makarantar zuwa ranar 20 ga watan Maris ko kafin nan.
Sannan jami’ar ta dakatar da duk wasu ayyukan da ake yi cikin jami’ar har sai makarantar ta dawo daga yajin aikin gaba daya, in ji Daily Trust.
A wata takarda wacce sakataren yada labaran jami’ar, Bala Abdullahi ya saki a maimakon magatakardar jami’ar, inda ya kula da cewa, wannan matakin ya biyo bayan kara watanni 2 da ASUU ta yi na yajin aikin ta.