fidelitybank

An tura tawagar ƙwararrun ƴan sanda su kuɓutar da Ɗalibai 20 da aka sace a Benue

Date:

Babban sifeton ‘yansandan ƙasa, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin tura ƙarin ƙwararrun jami’an rundunar zuwa jihar Benue, don taimakawa wajen kuɓutar da ɗaliban jami’ar da ‘yan bingida suka sace a jihar.

A ranar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka sace ɗaliban jami’ar Maiduguri da ta Jos, waɗanda ke kan hanyarsu ta zuwa jihar Enugu domin halartar wani taron shekara-shekara.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan ƙasar, Muyiwa Adejobi, ya fitar ranar Lahadi, ya ce Egbetokun ya bayar da umarnin tura ƙwararrun jami’an da kayan aiki, ciki har da jirage marasa matuƙa da masu saukar ungulu da motocin sulke domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban.

Mista Egbetokun ya kuma yi kira ga mazauna yankin su bayar da bayanan da za su taimaka wajen kuɓutar da ɗaliban.

Ya kuma jajanta wa iyalan ɗaliban tare da alƙawarta kuɓutar da su.

”Rundunar ‘yansanda na tare da iyalai da ‘yan’uwan ɗaliban a wannan lokaci na baƙin ciki da damuwa, kuma rundunarmu za ta yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da waɗannan ɗaliabi”, in ji sanarwar.

vanguardnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp