A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da tsohon ministan a gaban kuliya bisa zarge-zargen damfara a aikin samar da wutar lantarki na Mambilla.
A ranar Laraba ne aka gurfanar da Agunloye a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Sai dai alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali, har sai an yanke shawarar neman belinsa.