Usman Alkali Baba, Sufeto Janar na ‘yan sandan ƙasa a ranar Talata ya ce, za a tura jami’an ‘yan sanda 21,000, domin gudanar da zaben gwamnan jihar Osun a ranar 16 ga watan Yuli.
Alkali Baba ya bayyana haka ne a garin Osogbo a wurin taron masu ruwa da tsaki na zaben gwamna na Osun 2022.
Sai dai IGP din ya ce, an tura sojojin ne ba don a tsoratar da mazauna yankin ba, sai dai don hana miyagu yin garkuwa da mutane ko kuma kawo cikas ga shirin zaben.
Ya ce, jami’an da aka tura za su samar da tsaro, da kuma kare masu zabe, jami’an INEC da kayan aiki kafin zabe, lokacin da kuma bayan zabe.