An tuhumi tsohon shugaban Amurka, Donald Trump da yunƙurin murɗe zaɓen shekarar 2020 da ya sha kayi.
Ana zargin Trump da laifuka huɗu da suka haɗa da cin amanar ƙasa da lalata bayanan shaida da kuma yunƙurin tauye yancin ƴan ƙasa.
Zargin da ake masa ya biyo binciken da aka ƙaddamar ne kan zanga-zangar magoya bayansa a ginin majalisar Amurka ranar 6 ga watan Janairun 2021.
Mr Trump, ɗan shekara 77 yana fatan yin takara a zaɓen shugaban ƙasar mai zuwa kuma ya musanta laifin da ake zarginsa da su. In ji BBC.
A baya ma an zargi ɗan jam’iyyar Republican da ɓoye takardun bayanan sirri a gidansa da kuma bayar da bayanan ƙarya kan hada-hadar kasuwanci.
Binciken da aka yi kan zaɓen ya mayar da hankali ne kan matakan da Mr Trump ya ɗauka cikin watanni biyun ƙarshe na mulkinsa da kuma zanga-zangar birnin Washington inda magoya bayansa suka afkawa majalisar dokokin Amurka