fidelitybank

An tuhumar wani Asibiti a Kebbi bayan ɓacewar ƙunzugun Jarirai 13,350

Date:

Hukumar yaƙi da almundahana ta ICPC, ta ce, za ta binciki batun ɓacewar ƙunzugun yara da aka fi sani da Famfas kimanin 13,350 a ƙaramin asibitin shan magani da ke Sambawa a jihar Kebbi.

Shugaban hukumar, Dakta Musa Adamu Aliyu ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin taron da hukumar da shirya a Abuja.

Ya ce hukumar za ta yi bincike domin gurfanar da waɗanda ke da hannu a ɓacewar famfas ɗin.

Shugaban hukumar ya ce al’ummar Sambawan ne suka kai wa hukumar ƙorafin ɓacewar famfas ɗin da aka tanada domin tallafa wa masu juna biyu da jaririn da ake haifa a asibitin.

“Bincikenmu na farko ya nuna mana cewa yawan ƙunzugun da suka ɓace a asibitin ya kai 13,350, to amma binciken hukumar lafiya a matakin farko ta jihar Kebbi ya nuna adadin 3,466 ne”, in ji Adamu.

Ya ce akai mutum biyu mace da na miji da ke aiki da ƙaramin asibitin na Sambawa da ake zargi da hannu a ɓacewar tarin ƙunzugun. In ji BBC.

labaran duniya na yau

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp