Wani abin takaici ya faru a Kano, yayin da wani jariri ya fada a cikin rijiya da ke Ruguzau a karamar hukumar Takai a jihar.
Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar a ranar Laraba.
Ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.
“Mun sami kiran gaggawa da misalin karfe 02:14 na rana. daga wani Sabo Ladan cewa an tsinci gawar wani jariri yana shawagi a cikin rijiya.
“Nan take mun aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 02:18 na rana. Da isowar mutanenmu sun sami jariri a cikin rijiyar,” inji shi.
A cewarsa, an fito da jaririn daga rijiyar a sume kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.
Ya ce ana kan binciken lamarin.