An tsinci gawar kwamishinan kudi na jihar Borno Ahmed Ali Ahmed a dakinsa.
Duk da cewa har yanzu babu cikakken bayani kan lamarin, Aminiya ta ruwaito cewa an tsinci gawar kwamishinan ne bayan da aka bude kofarsa da karfi a safiyar ranar Litinin.
A cewar mazauna yankin, marigayin ya zarce lokacin da ya saba fitowa da safe, lamarin da ya kara janyo rade-radin cewa akwai matsala.
Gwamna Babagana Zulum ya rasa mambobin majalisarsa guda biyu cikin shekara guda.