An gano gawar wani ɗan jarida a Mexico da ya ɓace tun ranar Laraba a wani auye a jihar Nayarit da ke yammacın kasar.
Luis Martin Sanchez, mai shekaru 59, wakilin ɗaya daga cikin manyan jaridun Mexico, ne da ake kira La Jornada.
A cewar BBC, an tarar da gawarsa nannade a leda, sannan an samu wata wasiƙa da aka ɗaura a a ƙirjinsa.
Tun farko matarsa ce ta bada rahoton cewa wasu da ba a san ko su wane ne ba, sun kutsa har gidansu, tare da yin awon gaba da shi.
Mexico, na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi hadari ga ‘yan jarida a duniya, musamman masu ba da rahoto kan fataucin miyagun ƙwayoyi da cin hancı da rashawa