Majalisar dokokin jihar Cross River ta tsige kakakin majalisar Rt. Hon. Elvert Ekom Ayambem.
A ranar Laraba ne mambobin majalisar 17 daga cikin 25, suka amince da tsige kakakin nata sakamakon zarginsa da ɓarnatar da kuɗi.
Tun a ranar Talata ne ‘yan majalaisar suka fara yaunƙurin tsige kakankin, inda kusan ‘yan majalisar 20 suka goyi bayan ƙudirin tsige ɗan majalisar mai wakiltar ƙareamar hukumar Ikom 2.
A watan Yunin 2023 ne aka zaɓi Rt Hon Elvert Ayambem a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar ta 10.