Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka (CAF) ta ce, za a gudanar da gasar nahiyar ƙasashen Afirka ta Afcon a watannin Disamban 2025 da kuma Janairun 2026.
Hukumar Caf ta ce ƙasar Morocco ce za ta ɗauki nauyin gasar ta 2025 da za fara ranar 21 ga watan Disamban 2025 zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2026.
Gasar wadda ƙasashe 24 za su fafata za ta ci karo da lokacin da ake tsaka da gasar Premier.
Wannan ne karo na farko da za a buga gasar Afcon a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Haka kuma hukumar ta Caf ta sanar da ɗage gasar ƙwallon ƙafar mata ta 2024 zuwa watan Yulin shekara mai zuwa.
Gasar ta mata – wadda ita ma za a buga a Morocco – za a fara ta ne daga rabar 5 zuwa 26 ga watan na Yulin shekara mai zuwa.