Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya yi maraba da sanarwar kara dakatar da buɗe wuta da sojojin da ke yaki da juna a Sudan suka cimma ta ƙarin kwanaki uku.
Mr Blinken, ya yi kira ga sojin gwamnatin Sudan da dakarun RSF, da su mutunta wannan yarjejeniya da za ta ba da damar kai agaji da dubban ‘yan ƙasar da ke cikin halin tagayyara.
Amma tshohuwar ministar harkokin waje a Sudan, Maryam al Sadiq al Mahdi, da ta ke fakewa a gidansu da ke Khartoum, ta shaida wa BBC cewa har yanzu mazauna Khartoum na cike da firgici.
Ta ce dakatar da buɗe wutar ba ta da alaka da abin da ke faruwa, jirage na ci gaba da kai hare-hare, ana ci gaba da ruwan albarusai akan tituna