fidelitybank

An tsaurara tsaro gabanin fara sauraron shari’ar Gwamnan Nasara

Date:

An saka tsauraran matakan tsaro a harabar kotun daukaka kara da ke Abuja yayin da kotun za ta yanke hukunci a shari’ar zaben gwamnan jihar Nasarawa.

Jami’an tsaro dauke da muggan makamai daga rundunar ‘yan sandan Najeriya, da hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, da kuma jami’an tsaron farin kaya sun killace dukkanin hanyoyin da ke zuwa kotun daukaka kara.

Motoci masu zaman kansu da na ‘yan kasuwa da ke bin hanyoyin sakatariyar gwamnatin tarayya zuwa wurare daban-daban, an karkatar da su zuwa wasu hanyoyin tare da jami’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC, inda suka yi ta gwabzawa domin shawo kan cunkoson ababen hawa da suka samu kan hanyar.

Mahukuntan kotun ne suka aiwatar da matakan tsaron, kamar yadda jaridar DAILY POST ta tattaro, domin dakile yiwuwar karya doka bayan yanke hukunci.

Har zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoto, duka ma’aikatan kotun, lauyoyi, masu kara da kuma manema labarai suna ta kutsawa cikin babbar kofar shiga harabar kotun.

Duk da cewa an amince da wasu ‘yan jarida da dama da suka bayar da labarin yadda aka yanke hukuncin, biyar daga cikinsu ne kawai aka ba su damar shiga cikin dakin kotun saboda abin da wani jami’in kotun ya dorawa laifin rashin isasshen kujeru da kuma kula da jama’a.

Wakilinmu ya lura da cewa wasu daga cikin jami’an jam’iyyar siyasa da aka amince da su da masu goyon bayansu da suka isa kotun tun da karfe 8 na safe ne aka ba su izinin shiga harabar kotun, yayin da wasu da dama kuma ‘yan sandan tafi da gidanka dauke da makamai suka hana su zuwa nesa.

An dai gwabza kazamin fada tsakanin gwamna mai ci a jihar Abdullahi Sule na jam’iyyar APC da abokin hamayyarsa David Ombugadu na jam’iyyar PDP.

Idan dai ba a manta ba, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Nasarawa ta yanke hukunci mai rinjaye na biyu zuwa daya ta soke zaben gwamna Sule saboda rashin samun rinjayen kuri’un da aka kada a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Kotun ta bayyana Ombugadu, tsohon dan majalisar wakilai a matsayin wanda ya lashe zaben bisa ka’ida.

A halin yanzu dai ana dakon alkalai domin yanke hukunci.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp