fidelitybank

An tsaurara matakan tsaro a Abuja saboda zanga-zanga

Date:

Direbobi a kan babbar hanyar Keffi zuwa Abuja a ranar Litinin sun shiga tsaka mai wuya bayan da sojoji suka tare babbar hanyar domin gudanar da bincike kan motocin da suka nufi Abuja, babban birnin Najeriya.

Sojojin sun dasa shingen bincike a barikin sojoji na Sani Abacha kafin shataletalen AYA.

Jami’an tsaro dai ba su bayar da wata sanarwa ba kafin toshe titin lamarin da ya janyo cunkoson ababen hawa har zuwa gadar Nyanya, sama da kilomita 12 daga wurin binciken motocin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ma’aikata da masu tireda da ke aiki a Abuja, suna zaune a wajen tsakiyar birnin a wurare kamar Nyanya da Karu da Maraba da Masaka.

Bayan shafe tsawon sa’oi a wuri É—aya – babu gaba, babu baya, akasarinsu daga bisani sun yanke shawarar komawa gida.

Wasu matasa a Najeriya na shirya zanga-zangar gama-gari daga 1 ga watan Agusta saboda tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasar.

tribune

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp