Wani alƙali a birnin Magdeburg na ƙasar Jamus ya bayar da umarnin tsare wani ɗan ƙasar Saudiyyan da aka kama bisa zargin kai mummunan hari kan wata kasuwar Kirsimeti a birnin.
An gabatar da mutumin mai shekara 50 a gaban alƙali da maraicen ranar Asabar, bisa zargin tuƙo mota tare da kutsawa cikin kasuwar mai cike da cunkoson jama’a.
A wani taron manema labarai, mai gabatar da ƙara a birnin na Magdeburg, Horst Walter Nopens ya ce maharin shi kaɗai ya kitsa ya kuma kai harin.
Ya ce saɓanin rahotannin da ke ta yawo a shafukan sada zumunta a jiya, mai laifin mutum guda ne, kuma babu alamun akwai wani da ke aiki tare da shi.
Aƙalla mutum biyar ne suka mutu, da suka haɗa da mata uku da wani yaro mai shekara tara, yayin da sama da 200 suka jikkata a harin da aka kai da yammacin ranar Juma’a.