Akalla gawarwaki 18 ne aka gano yayin da wasu mutane shida suka bata, bayan da wani kwale-kwale ya kife a karamar hukumar Maiāadua ta jihar Katsina.
Wani mazaunin garin, Lawal Sakatare, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutane 24 da suke cikin jirgin yayin zuwa bikin Sallah a lokacin da ya kife, kuma mutane 18 wadanda yawancinsu kananan yara ne suka nutse.
āSha hudu daga cikinsu āyan kauyen Tsabu ne, hudu kuma āyan kauyen Dogon Hawa ne. An yi janaāizar 15 daga cikin 18 a Maiāadua a yau (Alhamis) yayin da sauran mutane shida da ke cikin jirgin suka bace,ā inji shi.
Ya kara da cewa, tawagar da ta fito daga kauyukan da lamarin ya shafa na ci gaba da aikin ceto sauran shidan, duk da cewa fatan samun su da rai ya dushe.
Kakakin rundunar āyan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, bai amsa kiran da aka yi masa ba a cewar Daily Trust, ko kuma ya amsa sakon tes da aka aike domin neman jin ta bakinsa kan lamarin.
A wani labarin kuma, wata motar jamiāan hukumar kwastam dake fafatawa da wasu da ake zargin masu fasa kwaurin ne a karamar hukumar Jibia ta Katsina ta murkushe mutum daya a ranar Laraba.
Wasu uku kuma sun samu raunuka a lamarin.
An bayyana cewa marigayin yana kan hanyarsa ta zuwa Katsina daga Jibia a kan babur, sai motar da ke gudu mai tsananin gudu ta farfasa shi.