fidelitybank

An tsamo gawar wasu Mata biyu da suka faɗa cikin kududufi a Kano

Date:

Wasu mata biyu sun rasa rayukansu a wani mummunan yanayi a karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano bayan da rahotanni suka ce sun fada cikin wani kududdufi a lokacin da suke kokarin wanke jikin su bayan aiki a wani kamfanin sarrafa zobo.

Lamarin wanda ya afku a yammacin ranar Litinin, an tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi ya raba wa manema labarai a ranar Talata.

A cewar sanarwar, hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 11:15 na safiyar ranar Talata daga kwamandan kungiyar ‘yan banga na yankin Gezawa, inda ya bayyana cewa matan sun shiga cikin kududdufin ne da nufin wanke gawarwakinsu bayan sun rufe bakin aiki.

Sanarwar ta ce “A cewar ‘yan uwansu ma’aikata ne a wani kamfanin sarrafa zobo ne suka shiga cikin ruwa da nufin wanke jiki bayan sun rufe bakin aiki, wanda hakan ya yi sanadin rasa rayukansu.”

Ko da yake an fara neman wadanda harin ya rutsa da su a yammacin ranar Litinin, amma sai da safiyar Talata aka tsinto gawarwakinsu. An same su a sume kuma aka mika su ga jami’in ‘yan sanda na Gezawa Musa Garba.

Hukumar kashe gobara ba ta bayyana sunayen wadanda suka mutu ba, kuma har yanzu ba a fayyace karin bayani kan yadda lamarin ya faru ba.

nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp