Hukumomi a Senegal sun toshe hanyoyin shiga shafukan sada zumunta da muhawara da suka hada da Facebook da WhatsApp sakamakon kazamin rikicin da ya biyo bayan hukuncin daurin shekara biyu da kotu ta yanke wa jagoran ‘yan hamayya na kasar.
Daman gwamnatin ta ce za ta dau duk wani mataki da ya dace domin kare rayuwar al’umma da dukiyoyi bayan mutuwar mutane sakamakon rikicin.
Akalla mutum tara ne suka mutu a rikici tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zanga, bayan yanke wa Ousmane Sanko hukuncin a jiya Alhamis.
Ministan cikin gida, Antoine Diome a wani taron ‘yan jarida a cikin dare, ya ce an toshe kafofin ne, yana mai nuna takaicin abubuwan da suka faru.
Rikicin ya fi baci a yankin Ziguinchor – (Zi-gan-shiyo)- da ke kudancin kasar, inda Mista Sonko ke rike da mukamin magajin gari.
Hukukuncin kotun da aka yanke a bayan idonsa na iya hana shi tsayawa takarar shugaban kasa a zaɓen shekara mai zuwa.
An same shi da laifin nuna rashin É—a’a, amma an wanke shi daga zargin aikata fyaÉ—e.


