Mutum 600 ne suka isa garin Dirkou jihar Agadez.ta Nijar bayan mahukunta sun koro su daga ƙasar Libya.
Hukumomin Dirkou ne da abokan hulɗarsu na hukumar Majalisa Ɗinkin Duniya da ke kula da baƙin haure suka tarbe su.
Da yawansu sun yi zaman gidan yari na tsawon watanni a Libya ba tare da shari’a ba.
“Watana biyar a gidan kaso kafin a kawo mu Nijar,” in ji wani daga cikinsu. Wani ma ya ce: “Mun sha wahala sosai. Ƙuraje sun fito min, mun sha wahala sosai.”
A ranar 1 ga watan Janairu ma bakin haure kimanin 770 ne suka isa Nijar din.
Mutanen da suka yi ta aika saƙonnin neman taimako saboda mawuyacin halin da suka fada a gidan yarin Gatrone da dama sun koma gida ɗauke da larura, yayin da mutum ɗaya ya rasu.
Jimillar ‘yan Nijar 1,300 ne suka isa ƙasar bayan koro su daga Libya, a cewar wakiliyar BBC Tchima Illa Issoufou.
Wani jami’in barikin da ya karɓi mutanen, Abare Abba Gana, ya ce dukka mutanen maza ne.