An harba wa magoya baya da ke makokin mutuwar fitaccen mawakin Afro MohBad a birnin Lagos, yayin da ‘yan sanda ke cewa masu taron suna tare hanya ga ababen hawa.
Sun taru ne a mashigin Lekki da ke tsakiyar birnin bayan wani bikin raye-rayen tunawa mutuwar mawakin mai shekara 27, wanda ya rasu makon jiya a wani asibitin Lagos.
Ana ta aika sakonnin alhini kan mutuwar mawakin da kuma neman a bayyana takamaimai abin da ya haddasa mutuwarsa ga jama’a.
Hukumomin Lagos a yanzu sun tono gawarsa a wani bangare na binciken da ake gudanarwa.
Raye-rayen an shirya su ne ranar Alhamis don juyayin MohBad, wanda ainihin sunansa shi ne Ilerioluwa Aloba, a wani dandali cikin Victoria Island.
Masu makokin sun sanya fararen riguna kuma sun rirrike kyandira ko kuma sun kunna fitilun wayoyinsu a lokacin da suke rawa ga wakokin marigayin, wanda ake nuna masa kauna saboda wayewar kansa da kuma wasu lokuta amfani da batsa a kade-kadensa da kuma fitacciyar barkekiyar muryarsa.
Taurarin mawaka kamar Davido da Falz da kuma Zlatan na cikin jerin mashahuran ‘yan fim din Nollywood, inda suka hadu don nuna jimamin mutuwar mawakin da ‘yan kallo


