Majalisar dattawa ta ci gaba da zaman tantance mutanen da shugaba Bola Tinubu ya aike mata don neman amincewa ya naɗa su ministoci.
A zaman na ranar Juma’a, majalisar ta fara ne da tantance tsohon gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola.
Wannan ne zaman majalisar na huɗu a kan wannan aiki na tantance ministoci.