Barr Bello Goronyo ya fito daga jihar Sokoto, kuma tsohon ɗan majalisar wakilan Najeriya ne.
Wasu daga cikin Sanatocin sun yi tambaya ga Hon Bello Goronyo, kan gudumuwar da zai bayar wajen magance matsalar tsaro da yankin da ya fito ke fuskanta.
Majalisar Dattijan Najeriya ta fara tantance mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya aika mata don neman amincewarta kafin ya naɗa su ministoci.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai aika da ƙarin sunaye, kamar yadda tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadi kowace jiha daga cikin 36 na kasar za ta samu akalla minista daya