Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo, Farfesa Farouk Adamu Kute, ya sanar da ɗage karɓa da tattara sakamakon zuwa ƙarfe 5:00 na maraice, bayan karɓar sakamakon ƙananan hukumomi 16.
Farfesa Kute ya ce za a tafi hutun ne kasancewar ragowar ƙananan hukumin biyu har yanzu ba su ƙarasa zauren tattara sakamakon zaɓen ba.
Kawo yanzu sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar APC mai hamayya a jihar ce kan gaba bayan da ta lashe ƙananan hukumomi 11, yayin da PDP mai mulkin jihar ke da rinjaye a ƙananan hukumo biyar.