Gwajin da ka yi wa shugaban Laberiya Joseph Boakai ya nuna cewa ba ya ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
Cikin makon da ya gabata ne shugaban ya yi gwajin da ya alƙawarta yi a lokacin da yake jawabi ga ‘yan majalisar ƙasar ranar 29 ga watan Janairu, mako guda bayan rantsar da shi.
Mista Boakai ya yi gwajin ne tare da mataimakinsa, Jeremiah Kpan Koung da sauran jami’an gwamnatinsa, ƙarƙashin kulawar ma’aikatar lafiyar ƙasar.
Shugaban ƙasar ya ce : “Matakin na daga cikin alƙawuran da na ɗauka na ƙoƙarin kawar da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a faɗin Laberiya”.
A lokacin da yake jawabi ga majalisar dokokin ƙasar, mista Boakai ya ayyana dokar ta ɓaci kan shan miyagun ƙwayoyi a ƙasar.
Shugaban ya kuma buƙaci duka jami’an gwamnatinsa da su gudanar da gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyin.