Hukumar kula da kwallon kafa ta Afirka, CAF, ta amince da soke matakin share fage na biyu na gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika.
Kungiyoyi 16 da suka yi nasara a zagaye na biyu na share fage za su haye kai tsaye zuwa matakin rukuni na gasar zakarun Turai.
An amince da sabuwar dokar yayin taron CAF na musamman a Morocco.
Zakaran gasar firimiya ta Najeriya sau tara Enyimba da Remo Stars za su wakilci Najeriya a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika ta CAF a kakar wasa mai zuwa.
Rivers United, tare da Bendel Insurance sun cancanci buga gasar cin kofin na CAF.


