An shawarci gwamnatin shugaba Ahmad Bola Tinubu da ta kara mai da hankali kan dangantakarta da kasar Rasha domin farfado da tattalin arzikin kasar.
A wata hira da manema labarai a Kano, fitaccen dan siyasar nan, Muhammadu Gambo Danpass, ya ce a fili yake cewa Jamhuriyar Rasha ta fi kowace kasa a yammacin duniya tsarin farfado da tattalin arzikin kasashen Afirka.
Danpass ya ce taron kasashen Afirka/Rasha da aka kammala kwanan nan da kuma sakamakonsa sun tabbatar da cewa Rasha ta fi daukar hankali wajen farfado da nahiyar Afirka.
Ya ce rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da kasashen Afirka sama da 40 da Rasha ta yi, ya nuna cewa kasar na nufin zaman lafiya ga nahiyar fiye da sauran wadanda ke sayar da harsashi ga bakar fata don yaki.
“Saboda haka, ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya kara ba da muhimmanci ga dangantakarmu da Rasha, domin gwamnatinsa ta gaggauta farfado da tattalin arziki don amfanin al’umma”.
Danpass wanda jigo ne a akidar Kwankwasiyya ta Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce gwamnatinsu a Kano nan gaba kadan za ta kara daukaka jihar.
Ya kuma yi kira ga ‘yan kasa da su yi hakuri da gwamnati domin nan ba da dadewa ba abubuwa za su daidaita.