Masu ruwa da tsaki a bangaren auduga, masaku da sutura a Najeriya, sun bukaci gwamnati da ta aiwatar da manufar taswirar masana’antu, wanda a ganinsu, yana da matukar muhimmanci ga farfado da fannin.
Shugaban kungiyar auduga ta kasa (NACOTAN), Achimugwu Anibe, ya ce, aiwatar da manufar zai kuma inganta alaka tsakanin masu ruwa da tsaki.
Masu ruwa da tsaki sun gana a wani taron karawa juna sani na kwana daya a Abuja, inda suka tattauna manufar CTG. Sun bayyana bukatar kara bunkasa noman auduga, karfin masana’antar ginshi da masaku a kasar.
An gudanar da taron ne tare da taimakon hukumar hadin gwiwa ta Jamus Deutsche Zusammennarbett, Tarayyar Turai (EU) da ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari ta Najeriya.
Sauran manyan masu ruwa da tsaki sun hada da kungiyar dillalan auduga ta Najeriya (COPMAN), kungiyar masu sana’ar kayan masarufi ta Najeriya (NTMA) da kuma Cotton Ginners (GAMAN).
Babban bankin kasa CBN a shekarar da ta gabata ya bayyana shirin farfado da fannin. Shirin dai shi ne zai baiwa kasar damar dogaro da kanta wajen noman auduga da kuma samar da ayyukan yi, tare da inganta kwarewar ‘yan Najeriya a kan darajar noman auduga.
A baya Najeriya na da kusan masana’anta 52, amma 21 ne kawai ke aiki a yanzu.
A sakamakon haka, ton 100 na auduga ne ake sarrafawa a duk shekara maimakon tan 600, inji Anibe.