Tsohon dan takarar gwamnan Kano, Malam Sha’aban Ibrahim Sharada, ya sasanta rikicin da aka shafe sama da shekaru 30 ana yi kan makarantar Islamiyya da masallacin Sharada.
An dauki lokaci mai tsaho ana wannan takaddamar tsakani Alhaji Shehu Uba Sharada da Dagacin garin Sharada Alhaji Iliyasu Ma’azu, da ya ke wakiltar al’ummar unguwar, da ta kai an kai kararraki sama da 100 a kotuna daban daban.
Taron sulhun ya gudana ne a daren Alhamis a gidan Hon. Sha’aban Sharada da aka shafe kimanin awanni 3 ana tattaunawa, da har ta kai an cimma matsaya da kuma samar da sulhu ga bangarorin biyu.
Dukkanin bangarorin sun yafi juna, yayinda suka tabbatar da cewa sabanin da ke tsakaninsu ya zo karshe. Kamar yadda Malam Sha’aban Ibrahim Sharada ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Zaman sulhun ya samu halartar wakilan bangarorin biyu, da bangaren masaurata karkashin jagorancin Dallatun Kano Hakimin Gundummar Sharada Malam Mahe Bashir, da kuma baturen ‘yansanda na chaji ofis din Sharada CSP. Abdurrahim Adamu, da ma sauran masu ruwa da tsaki na unguwar ta sharada