fidelitybank

An sassara dan shekara 12 gunduwa-gunduwa a Zaria

Date:

Wasu da ba a san ko su waye ba sun kashe wani yaro mai suna Abdulkadir dan shekara 12 a Zariya.

Marigayi Abdulkadir, mazaunin Madarkaci, an ce ya gamu da ajalinsa ne a ranar Litinin, lokacin da aka tura shi ya karbi waya daga a wajen masu caji a kasuwanci da ke kusa, amma bai dawo ba.

A cewar mahaifinsa, Aminu Saleh Muhammad, an gano gawar Abdulkadir da aka yanke a wani gini da ba a kammala ba a yankin.

Wata majiya ta bayyana cewa mahaifin marigayin, Aminu, ya yi zargin cewa wadanda suka kashe shi ‘yan ibada ne, yana mai jaddada cewa, “sun yanka shi ne ta hanyar cire masa idanuwa, al’aurarsa, harshensa kuma suka karya masa kafarsa, tare da tsage masa kwanyarsa.”

Mahaifin ya nemi gawar daga hannun ‘yan sanda domin binne gawar.

An binne gawar yaron kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

DSP Muhammad Jalige, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wasu da ba a san ko su wanene ba ne suka yanka yaron har lahira.

Jami’in hulda da jama’a ya ce, tuni ‘yan sanda suka fara bincike a kokarin ganowa tare da cafke wadanda suka aikata laifin domin fuskantar fushin doka.

latest news nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp