Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar Labour Party a jihar Abia, Mista Maduka Zachary.
Rahotanni na cewa an kashe jigon jam’iyyar wanda ya rike mukamin Darakta Janar na yakin neman zaben LP a mazabar Isuikwuato Umunneochi na tarayya a zaben da ya gabata a gidansa da ke Uturu a karamar hukumar Isuikwuato ta jihar.
‘Yan bindigar, a cewar rahotanni, sun kai farmaki gidan marigayin ne a ranar Laraba, inda suka kashe shi tare da sare masa kai.
Sai kawo yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Abia ya ba ta ce komai ba a kan wannan lamari.


